Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu

Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu

Daga Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe alhariri da hagunsa, kuma zinare da damansa, sannan ya ɗaga hannayensa da su, sai ya ce: "Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu".

[Ingantacce ne duka Riwayoyin nasa guda biyun] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe wani tufafi na alhariri ko wani yanki daga gare shi, da hannunsa na hagu, kuma ya riƙe zinariya ta ado ko mai kama da ita, da hannunsa na dama, sannan ya ce: Lallai alhariri da zinariya, sanya su haramun ne akan maza, amma mata to su halal ne garesu.

فوائد الحديث

AlSindi ya ce: (Haramun): Abin nufi yin anfani da su a sawa; inba haka ba ai yin anfani canji da ciyarwa da siyarwa ya halatta, yin anfani da zinariya ta hanyar sarrafata kwanuka da yin anfani da su to haramun ne.

Yalwar shari'ar musulunci ga mata dan buƙata zuwa ga ado da makancinsa.

التصنيفات

Kaya da kuma Ado