Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce

Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce

Daga Abul Haura'u al-Sa'adi ya ce: Na cewa Hassan ɗan Ali - Allah Ya yarda da su -: Me ka haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -? ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce".

[Ingantacce ne]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abinda kake kowanto a cikinsa na maganganu da ayyuka cewa shi an hana ne koko a'a, shin shi haramun ne ko halal ne, zuwa abinda babu kokwanto a cikinsa daga abinda ka sakankance kyansa da kuma halaccinsa, domin cewa zuciya zata nutsu gare shi ta samu kwanciyar hankali, abinda kuma a cikinsa akwai kokwanto to zuciya tana kaikawo daga gareshi kuma tana raurawa.

فوائد الحديث

Ya wajaba akan musulmi ya gina al'amuransa akan yaƙini da barin abinda ake kokwanto a cikinsa, kuma ya zama mai basira akan Addininsa.

Hani daga afkawa cikin shubuhohi.

Idan kana son nutsuwa da hutu to kabar abinda ake kokwanto a cikinsa ka jefar da shi a gefe.

Rahamar Allah ga bayinSa dan Ya umarcesu da abinda a cikinsa akwai hutun rai da zuciya, kuma ya hanesu daga abinda a cikinsa akwai raurawar zuciya da kuma ɗimuwa.

التصنيفات

Cinkaro da kuma zavar wanda ya fi inganci