إعدادات العرض
Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa
Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa
Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी বাংলা Español Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە دری Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Soomaali Moore Українська Български Tagalog Wolof Azərbaycanالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah, sai su zama kamar maƙabartu, da ba a sallah a cikinsu. Sannan sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labarin shaiɗan yana ficewa daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara.فوائد الحديث
Ana so a yawaita ibada da Sallolin Nafila a gidaje.
Ba ya halatta yin Sallah a maƙabarta, domin hakan hanya ce daga hanyoyin shirka da wuce iyaka ga masu su, in banda sallar Janaza.
Hanin yin Sallah a inda akwai kabari, ya tabbata a wurin Sahabbai, saboda haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana a sanya gidaje kamar maƙabartu, waɗanda su ba a Sallah a cikinsu.
التصنيفات
Falalar Surori da Ayoyi