Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya

Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya

Daga Dawus cewa shi ya ce: Na riski wasu mutane daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna cewa kowane abu (yana kasancewa) da kaddara ne, ya ce: Na ji Abdullahi Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su, yana cewa: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya ".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa kowanne abu da kaddara ne; Har kasawa: ita ce: Barin abinda yake wajibi ne aikata shi, da cewa zai yi ta jinkirta shi daga lokacinsa, da al'amuran duniya da lahira. Har dabara ita ce: Nishadi da kwarewa da al'amuran duniya da lahira. Kuma cewa Allah - Mai girma da daukaka - hakika Ya kaddara gajiyawa da wayo da kowane abu, ba zai afku a kasantacce ba sai hakika sanin Allah Ya rigaya da shi da mashi'arSa.

فوائد الحديث

Bayanin kudircewar sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kaddara.

Kowanne abu yana faruwa ne da kaddarawar Allah har gajiyawa da kuma nishadi.

Ya tabbata kuma sahabbai - Allah Ya yarda da su, sun tsoratar - a cikin riwayar hadisan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

Yin imani da kaddara dukkaninsa alherinSa da kuma sharrinSa.

التصنيفات

Imani da Hukuncin Allah da Qaddara, Matakan Hukuncin Allah da Qaddara