Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, ku ce: {Mun yi imani da Allah da abinda aka saukar mana}

Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, ku ce: {Mun yi imani da Allah da abinda aka saukar mana}

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mazowa littafi sun kasance suna karanta Attaura da Ibirananci, kuma suna fassarata da larabci ga ma'abota Musulunci, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, ku ce: {Mun yi imani da Allah da abinda aka saukar mana} [Al-Baqara: 136] Aya".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar da al'ummarsa daga ruduwa da abunda mazowa littafi suke ruwaitowa daga littattafansu, Yayin da Yahudawa suka kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna karanta Attaura da harshen ibirananci, shi ne harshen Yahudawa, kuma suna fassarata da larabci, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ku gasgata mazowa littafi kuma kada ku karyatasu, wannan a cikin abinda ba'a gane gaskiyarsa daga karyarsa; Wannan domin cewa Allah - Madaukakin sarki - Ya umarcemu mu yi imani da abinda aka saukar agaremu na Alkur’ani , da abinda aka saukar garesu na littafi, saidai cewa shi babu wata hanya garemu zuwa musan ingancin abinda suke hakaitowa daga wadancan littattafan da kuma mara kyansa, idan abinda zai bayyana gaskiyarsa daga karyarsa bai zo a shari'armu ba, Sai mu tsaya, Ba zamu gasgata su ba; dan kar mu zama abokanan tarayya tare dasu a cikin abinda suka canza shi, kuma kada mu karyatasu; watakila zai iya zama ingantacce, sai mu zama masu musun abinda aka umarcemu da mu yi imani da shi. Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni mu ce: {Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãka da Ya'aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabẽwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne}. [Al-Baqara: 136].

فوائد الحديث

Abinda mazowa littafi suka bada labarin shi ya rabu gida uku:

Akwai bangaren da ya dace da Alkur’ani da sunna sai agasgatashi.

Da bangaren da ya sabawa Alkur’ani da sunna to wannan batacce ne kuma za'a karyatashi.

Da kashi na uku babu abinda yake nuni akan gaskiyarsa ko karyarsa a cikin Alkur’ani da sunna; to wannan za'a ruwaitoshi, ba za’a gasgatashi ko a karyatashi ba.