Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne

Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne

Daga Uqubah Dan Amir Al-Juhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne".

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mai bayyanar da karatun Alkur’ani kamar mai bayyanar da bayar da sadaka ne, mai boye karatun Alkur’ani kamar mai boye bayar da sadaka ne.

فوائد الحديث

Boye karatun Alkur’ani shi ya fi , kamar yadda boye sadaka shi yafi, dan abinda yake cikinsa na tsarkake niyya da nisanta daga riya da jiji da kai, sai dai idan bukata da maslaha sun bukaci bayyanarwar kamar koyar da Alkur’ani .

التصنيفات

Falalar al-qur'ani Maigirma, Falalar al-qur'ani Maigirma, Falalar Ayyukan Zukata, Falalar Ayyukan Zukata, Ladaban Karatun Al-qur'ani, Ladaban Karatun Al-qur'ani