إعدادات العرض
Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya
Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya
Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya, Allah - Mai girma da daukaka - Zai ce da su a ranar Alkiyama idan za’a yi wa mutane sakayyar ayyukansu: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna nuna musu ayyukanku a duniya, sai ku duba shin zaku samu wani sakamako a wurin su?".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá සිංහල தமிழ் ไทย دری Кыргызча or Kinyarwanda नेपाली Română Malagasy Lietuvių Oromoo Nederlands Soomaali Српски Українська ಕನ್ನಡ Wolof Moore ქართული Azərbaycan Magyar Македонскиالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafi yawan abinda yake jin tsoronsa ga al'ummarsa: Karamar shirka ita ce: Riya; Ita ce ya yi aiki saboda mutane. Sannan ya bada labari game da ukubar masu riya a ranar Alkiyama za’a ce da su: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna aiki saboda su, ku duba shin suna mallakar saka muku da baku lada akan wannan aikin?!فوائد الحديث
Wajabcin tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da daukaka - da gargadarwa daga riya.
Tsananin tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, da kwadayinsa akan shiriyarsu da kuma nasiharsa garesu.
Idan wannan ya zama shi ne tsoronsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi alhali shi yana yiwa sahabbansa magana kuma su ne shugabannin salihai to tsoro akan wanda ke bayansu ya fi tsanani.