إعدادات العرض
Ka Guji Duniya Sai Allah ya so ka, ka guji abin hannun Mutane sai Mutane su so ka
Ka Guji Duniya Sai Allah ya so ka, ka guji abin hannun Mutane sai Mutane su so ka
Daga Sahal Dan Sa'ad Al'sa'idi Allah ya yarda da shi ya ce: wani Mutum ya zo wajen Annabi sai ya ce ya Manzon Allah, Nunamun wani akiki idan nayi shi Allah zai so ni kuma Mutane Ma zasu so ni sai ya ce "Ka Guji Duniya Sai Allah ya so ka, ka guji abin hannun Mutane sai Mutane su so ka"
[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português සිංහලالشرح
Wani Mutum ya zo wajen Annabi yana neman ya shiryar da shi izuwa wani aiki da idan yayi shi zai zamanto masa sanadin samun soyayyar Allah da kuma soyayyar Mutane, sai Annabi ya shiryar da shi, izuwa wani aiki wanda ya tattare komai zai samar masa da soyayyar Allah da kuma soyayyar Mutane, sai Annabi ya ce: "Ka guji Duniya" ai kada ka nemi komai a cikinta sai abinda kake bukatarsa kuma duk abinda baka bukata ka rabu da shi, da kuma duk abinda ba zai maka amfani ba a lahira, kuma kayi tsansteni da duk abinda zai cutar da Addininka, kuma ka nisanci abin duniya da mutane suke ta rubibin nema, to kuma idan ya kasance akwai wani abu a tsakaninka da dayansu wani abu ko kuma wani ciniki to ka kasance kamar yadda Annabi ya fada: "Allah yaji kan wani Mutum Mai sauki idan ya siyar kuma mai sauki idan ya zo siya, haka mai sauki idan zai biya, kuma mai saukin kai idan zai nemi a biya shi"; don ka zamanto abin so a wajen Allah.التصنيفات
Zuhudu da tsantseni