Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita

Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita

Daga Salim ɗan Abulja'ad ya ce: Wani mutum ya ce: Ina ma dai na yi sallah in huta, kamar cewa su (sauran mutanen) sun aibata masa hakan, sai ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita".

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Wani mutum daga sahabbai ya ce: Ina ma na yi sallah in huta, kai ka ce waɗanda ke gefensa sun aibata hakan gare shi , sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Ya kai Bilal! ka kira sallah ka yi iƙamarta; don mu samu hutu da ita; saboda abin da ke cikinta na ganawa da Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma hutu ga rai da zuciya.

فوائد الحديث

Hutun zuciya yana kasancewa ne da yin sallah; saboda abin da ke cikinta na ganawa da Allah - Maɗaukakin sarki -.

Inkari a kan wanda ya ke yin nauyin (jiki) game da ibada.

Wanda ya ba da wajibin da yake a kansa, ya kuɓutar da wuyayensa daga shi, hutu zai tabbata ta hakan gare shi da samun nutsuwa.

التصنيفات

Falalar Sallah, Kiran Sallah da Iqama