إعدادات العرض
Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta
Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta".
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी বাংলা Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá ئۇيغۇرچە ไทย دری Кыргызча or Kinyarwanda नेपाली Română Lietuvių Malagasy ಕನ್ನಡ Oromoo Nederlands Soomaali Српски Українська Wolof Moore ქართული Azərbaycan Magyarالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa da Allah cewa wani daya daga wannan al'ummar ba zai ji shi ba, Bayahude ne ko Kirista ko waninsu (ba zai ji) kiran Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya isa zuwa gare shi ba, sannan ya mutu bai yi imani da shi ba sai ya zama daga 'yan wuta yana madawwami a cikinta har abada.فوائد الحديث
Gamewar sakon Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zuwa dukkanin halittu, da wajabcin binsa, da shari'arsa ta shafe dukkanin shari'o'i.
Wanda ya kafirce da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi - ikirarins na imani da waninsa daga Annabawa - tsira da aminci ya tabbata agare su baki daya - ba zai amfanar da shi da komai ba.
Wanda bai ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba, kuma sakon musulunci bai isa zuwa gare shi ba to shi yana da uzuri, al'amarinsa a lahira yana ga Allah - Madaukakin sarki -.
Amfanuwa da musulunci yana tabbata koda kafin mutuwa ne, koda a halin tsananin rashin lafiya ne, muddin dai rai bai kai makogwaro ba.
Inganta Addinin kafirai - daga cikinsu akwai yahudawa da kiristoci - kafirci ne.
Ambaton yahudawa da kiristoci - a cikin hadisin - dan fadakarwa ne akan wasunsu; hakan domin cewa yahudawa da kiristoci suna da littafi, idan hakan ya zama sha'aninsu, to wasunsu daga wadanda ba su da littafi ya fi cancanta, dukkaninsu shiga Addininsa da biyayya gareshi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zama dole akansu.
التصنيفات
Annabinmu Muhammad SAW