Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna

Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna

Daga Ma'aƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Babu wani bawa da Allah Zai ba shi kulawar wani abin kiwo, ya mutu a ranar da zai mutu alhali shi yana algus ga abin kiwonsa sai Allah Ya haramta masa aljanna".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ba da labarin cewa kowane mutumin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanyashi majiɓinci, kuma shugaba ga mutane, duk ɗaya ne ya kasance shugabanci ne mai gamewa kamar sarki, ko keɓantaccen shugabanci ne kamar mutum a gidansa da mace a gidanta, sai ya gaza a haƙƙin waɗanda aka ba shi kiwonsu, ya yi musu algus bai yi musu nasiha ba, sai ya tozarta haƙƙoƙinsu na addini da na duniya, to, haƙiƙa ya cancanci wannan uƙubar mai tsanani.

فوائد الحديث

Wannan narkon bai keɓanci babban shugaba ba da mataimakansa, kai, shi mai gamewa ne a dukkanin wanda Allah Ya ba shi kiwon wani abin kiwo.

Wajibi a kan dukkanin wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin musulmai ya yi musu nasiha, kuma ya yi ƙoƙari wajen ba da amana, kuma ya kiyayi ha'inci.

Girman nauyin da ke wuyan dukkanin wanda ya jiɓinci wani abin kiwo mai gamewa, ko keɓantacce, babba ne ko ƙarami ne.

التصنيفات

Manufofin shari'a