Ku riskar da gado ga masu shi,abin da yayi saura to na namiji mafi kusa da mamaci ne

Ku riskar da gado ga masu shi,abin da yayi saura to na namiji mafi kusa da mamaci ne

Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda dasu- Daga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi: " ku riskar da gado da masu shi, abin da yayi saura kuma to na mafi kusa da mamacin ne" A wata ruwayar: "ku raba dukiya tsakanin magada bisa yadda littafin Allah ya raba, abin da yayi saura to na mafi kusa da mamacin ne".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya umarci masu raba gado dasu raba wa wadanda suka cancanci rabon bisa adalci kamar yadda sharia tayi bayani. sai abaiwa magada abin da Allah ya kaddarawa kowa a cikin Littafinsa, shi ne Biyu cikin uku, da Daya cikin uku, da Daya cikin shida, da Rabi, da Daya cikin hudu, da Daya cikin takwas. Abin da yayi saura bayan wannan, to sai a baiwa mafi kusanci da mamacin daga maza; shi ake cewa Asaba.

التصنيفات

Asibai