'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin

'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin

Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin munafiki kuma shi kamar akuya ce mai kaikawo, ba ta san wanne garke za ta bi ba na tumakai, Tana tafiya zuwa wannan garken wani lokaci, da kuma zuwa wani garken a wani lokacin daban, Su masu dimuwane tasakanin imani da kafirci, su ba sa tare da muminai a zahiri da badini, kuma su ba sa tare da kafirai a zahiri da badini, su dai zahirinsu suna tare da muminai, kuma badininsu suna cikin kokwanto da taraddudi, wani lokaci yana karkata zuwa ga wadannan, wani lokacin kuma zuwa ga wadannan.

فوائد الحديث

Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - buga misali dan kusanto da ma'anoni.

Bayanin halin munafikai na kaikawo da kokwanto da rashin tabbas.

Gargadi akan halin munafikai, da kwadaitarwa akan gaskiya da kudirin niyya a kan imani a zahiri da badini.

التصنيفات

Munafunci