Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta

Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku isar game da ni koda aya daya ce, kuma ku zantar game da Banu Isra'ial babu laifi, duk wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi mazauninsa a wuta".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umarni da isar da ilimi daga gare shi na littafi ne ko Sunnah, koda abin ya zama kadan ne kamar aya daya daga Alkur’ani ko hadisi, da sharadin ya zama masani da abinda zai isarda shi kuma ya yi kira zuwa gare shi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa babu laifi da akan bayanai daga Banu Isra'il da abinda ya afku gare su na al'amura da abinda ba ya karo tare da shari'a. Sannan ya yi gargadi daga yi masa karya, kuma cewa duk wanda ya yi masa karya da gangan to yariki masauki a wuta.

فوائد الحديث

Kwadaitarwa a isar da shari'ar Allah, kuma cewa mutum ya zama dole akansa ya bayar da abinda ya haddace kuma ya fahimta koda ya zama kadan ne.

Wajabcin neman ilimi na shari'a dan ya samu ga tabbata ga bautar Allah da kuma isar da shari'arSa da inagantacciyar sura.

Wajabcin tabbaci daga inagancin kowanne Hadisi kafin isar da shi ko yadashi dan kiyayewa daga shiga a wannan narkon mai tsanani.

Kwadaitarwa akan gaskiyar zance da kuma kiyayewa a Hadisi dan kada ya afka a cikin karya, musamman ma a shari'ar Allah - Mai girma da daukaka -.

التصنيفات

Muhimmancin Sunna da Matsayinta, Hukuncin kira Zuwa ga Allah