Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi

Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya ziyarci Dakin Allah - Madaukakin sarki - da Hajji kuma bai yi kwarkwasaba, kwarkwasa ita ce jima'i da abubuwan dake da alaka da shi na sumbata da runguma, kuma ana ambatansa da mummunanan zance, kuma bai yi fasikanciba, ta hanayar aikata sabo da munanan ayyuka ba, Daga fasikanci akwai aikata abubuwan da ka haramta in an yi harama, zai dawo daga hajjinsa wanda aka gafartawa, kamar yadda ake haifar yaro kubutacce daga zunubai.

فوائد الحديث

Fasikanci koda ya kasance abin hanawa a kowane lokaci, to hanin yana karfafuwa a aikin hajji dan girmamawa ga ayyukan Hajji.

Mutum ana haifarsa ba tare da kurakurai ba kubutacce daga zunubai; to shi ba ya daukar kuskuren waninsa.

التصنيفات

Falalar Hajji da Umra