إعدادات العرض
Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka
Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji wani mutum yana cewa: A'a na rantse da Ka'abah, sai Dan Umar ya ce: Ba'a rantsuwa da wanin Allah, domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka".
[Ingantacce ne]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands සිංහල தமிழ் ไทย دری Akan Български Fulfulde Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy नेपाली or Română Kinyarwanda тоҷикӣ O‘zbek Azərbaycan Moore Wolof Oromoo Soomaali Українська bm km rn Српски ქართული Македонскиالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.فوائد الحديث
Lallai cewa girmamawa da yin rantsuwa hakki ne na Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayenSa da siffofinSa.
Kwadayin sahabbai akan horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki, musamman ma idan abin kin ya kasance daga abinda yake rataya ne da shirka ko kafirci.
التصنيفات
Shirka