إعدادات العرض
Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku
Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku
Daga Abdullahi Dan Shikkhir - Allah Ya yarda dashi - ya ce: Na tafi a cikin jama'ar Banu Amir zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Kiswahili Português සිංහල Svenska ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Tiếng Việt پښتو অসমীয়া دری Кыргызча or नेपाली Malagasy తెలుగు Čeština Oromoo Română Kinyarwanda മലയാളം Nederlands Soomaali ไทย Lietuvių Српски Українська Shqip ಕನ್ನಡ Wolof ქართული Moore Azərbaycan Magyarالشرح
Wasu jama'a suka zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka iso wurinsa sai suka fadi - suna masu yabonsa - wasu daga cikin kalmomin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ki su, sai suka ce ; "Kai ne shugabanmu", sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shugaba (Shi ne) Allah" Cikakken shugabanci nasa ne akan halittarSa su bayinSa ne. Suka ce : Kai ne "Mafificinmu a fifiko" kuma mafi daukakarmu a daraja da daukaka. kuma kaine "Mafi girmanmu a kyauta" mafi yawaitawarmu a kyauta da daukaka da daraja. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nuna musu su fadi maganarsu ta al'ada kada su kallafawa kansu lafazai, kuma kada Shaidan ya Ja su zuwa wuce gona da iri da kanbawar da zata afkar cikin abinda aka haramta na shirka da hanyoyinta.فوائد الحديث
Girman darajar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a rayukan sahabbansa da girmamawarsu gare shi .
Hani daga matsama kai a lafazi, da takaituwa a magana.
Kariya ga Tauhidi daga abinda zai bata shi na maganganu da ayyuka.
Hani daga wuce gona da iri a yabo, shi yana daga hanyoyin Shaidan,
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ne shugaban 'ya'yan Adam, abinda ya zo a hadisi shi yana babin kankar da kai ne, kuma a babin tsoro garesu kar su fada a wuce iyaka.
التصنيفات
Annabinmu Muhammad SAW