Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi

Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi

Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari, Cewa cikakken mutum a sada zumunci da kuma kyautatawa 'yan uwa shi ne mutumin da yake fuskantar kyakkyawa da kyakkywa, Kai mai sadarwa a hakika a sada zumunci shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi, idan sun munana masa to sai shi ya fuskantarsu da kyautatawa zuwa garesu.

فوائد الحديث

Sada zumunci abin la'akari a shari'a shi ne ka sadarwa wanda ya yanke maka daga gare su, ka yi afuwa ga wanda ya zalinceka, ka bawa wanda ya haramta maka, bawai sadarwar fuskanta da sakayya ba.

Sada zumunci yana kasancewane ta hanyar sadar da abinda zai yiwu na alheri na dukiya da addu'a, da horo da aikin alheri, da kuma hani daga abin ki da makamantansu, da kuma tunkude abinda zai yiwu na sharri daga gare su.

التصنيفات

Al-ummar Musulmai