إعدادات العرض
Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci
Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci
Daga Abu Buraidah Ɗan Husaib, Allah ya yarda da shi ya ce: Ku gaggauta sallar La’asar a kan lokaci, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci.
[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी বাংলা Español Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ ไทย Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە دری Magyar Italiano ಕನ್ನಡ Кыргызча Lietuvių Malagasy Română Kinyarwanda नेपाली Српски Wolof Soomaali Moore Українська Български Tagalog Azərbaycan ქართული тоҷикӣ bm Македонскиالشرح
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsawatar a kan jinkirta sallar La’asar daga lokacinta da gangan, kuma duk wanda ya yi hakan, to, aikinsa ya lalace, ya tafi kawai a watse.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa a kan kiyaye sallar la’asar a farkon lokacinta, da kuma gaggawar yinta.
Narkon azaba mai tsanani ga wanda ya bar sallar La’asar har loakcita ya fita, kuma barinta har fitar Lokacita ya fi tsanani a kan wata da ba ita ba, domin ita ce Sallah mafificiya wacce aka keɓance ta da umarni a faɗin Allah maɗaukaki: ((Ku kiyaye Salloli kuma ku kiyaye sallah mafificiya)). Bakara, 238.