إعدادات العرض
Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in
Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta ana samunsa daga (tsawon) tafiyar shekara arba'in".
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Русский हिन्दी Bahasa Indonesia 中文 বাংলা اردو Español Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் සිංහල မြန်မာ ไทย 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands ئۇيغۇرچە Türkçe دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली Italiano or ಕನ್ನಡ Oromoo Română Soomaali Српски Wolof Українська Tagalogالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana narko mai tsanani a kan wanda ya kashe kafirin amana - shi ne kafiri wanda ya shiga garin musulunci bisa alƙawari da amincin - cewa ba zai shaƙi ƙamshin aljanna ba, kuma ƙamshinta yana kasancewa ne a kan nisan tafiyar shekara arba'in.فوائد الحديث
Haramcin kashe kafirin amana da zimmi da musta'aman (wanda aka ba shi amincin ɗan wani lokaci) daga kafirai, kuma cewa hakan babban laifi ne daga manyan laifuka.
Kafirin amana: Shi ne wanda aka yi alƙawari da shi daga kafirai a kan ya zauna a garinsa ba zai yaƙi musulamai ba su ma ba za su yaƙe shi ba. Zimmi kuma: Shi ne wanda ya zauna a garin musulmai ya ba da jizya. Musta'aman kuma: Shi ne wanda ya shiga garin musulmai a kan alkawari da aminci na wani ƙayyadajjen lokaci.
Gargaɗi daga ha'intar alƙawurra (da aka ƙulla) tare da wanin musulmai.
التصنيفات
Hukunce hukuncen Kafiran Amana