Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya

Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Abdullah ɗan Amr - Allah Ya yarada da su - ya ce: Na kasance ina rubuta dukkanin abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - don na haddace shi a rubuce, sai wasu mutane daga Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin yarda da fushi, zai iya yin kuskure, sai na daina rubutun. Sai na ba wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - labarin abin da suka faɗa, sai ya yi nuni da danyatsansa zuwa bakinsa, sai ya ce; Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da yake fita daga cikinsa sai gaskiya a kowanne hali, haka a halin yarda da fushi. Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ba ya magana bisa son rai* shi (Alƙur'ani) ba wani abu ba ne ba ban da wahayi da ake saukar masa) [Al-najm 3-4].

فوائد الحديث

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ma'asumi (wanda ba ya laifi, kuma ba ya kuskure) ne a cikin abin da yake isar da shi daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - a halin yarda da fushi.

Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kan kiyaye sunna da isar da ita.

Halaccin rantsuwa ko da ba a sa a yi rantsuwar ba don maslaha, kamar ƙarfafa wani al'amari.

Rubuta ilimi yana daga mafi muhimmancin dalilai da suke kiyaye ilimi.

التصنيفات

Muhimmancin Sunna da Matsayinta, Rubuta Sunnar Annabi, Annabinmu Muhammad SAW