Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado

Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Jibrilu bai gushe ba yana maimaita masa kuma yana umartarsa da kulawa da maƙoci, wanda shi ne makusancin gida, musulmi ne ko kafiri, ɗan uwa ne ko ba ɗan uwa ba ne, da kiyaye haƙƙinsa da rashin cutar da shi, da kyautatawa gareshi da haƙuri a kan cutarsa, har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi zaton cewa daga girmama haƙƙin makoci da maimaitawar Jibrilu hakan cewa wahayi zai sauka da a ba shi (wani abu )daga dukiyar maƙocinsa wacce zai barta bayan mutuwarsa.

فوائد الحديث

Girman haƙƙin maƙoci da wajabcin kula da hakan.

Ƙarfafawa a kan haƙƙin maƙoci da wasiyyarr da take hukunta larurar girmamashi da nuna soyayya da kyautatawa zuwa gareshi, da tunkuɗe cutarwa daga gareshi, da dubo shi a yayin rashin lafiya, da tayashi murna a yayin farin ciki, da yi masa ta'aziyya a yayin musiba.

A duk lokacin da ƙofar maƙoci ta zama mafi kusa, to, haƙƙinsa ya zama mafi ƙarfi.

Cikar shari'a a cikin abin da ta zo da shi na gyaran zamatakewa wajen kyautatawa maƙota da tunkuɗe cuta daga garesu.

التصنيفات

Sulhu da Hukunce Hukuncen Maqwabtaka