إعدادات العرض
Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata
Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata
Daga Samura ɗan Jundub da Mugira ɗan Shu'ubah - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata".
[Ingantacce ne]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Kurdî Português සිංහල অসমীয়া Kiswahili Tiếng Việt አማርኛ ગુજરાતી Nederlands پښتو नेपाली ไทย മലയാളം Кыргызча Română Malagasy Svenskaالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda ya riwaito wani Hadisi daga gare shi alhali shi yana sane ko yana zato ko yana rinjayar da zatansa cewa shi Hadisin ƙaryane a gare shi- tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; to maruwaicinsa yana tarayya da mai ƙirƙirar wannan ƙaryar.فوائد الحديث
Tabbatar da Hadisan da aka ruwaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da tabbatar da ingancinsu kafin ruwaitosu.
Siffar ƙarya ana sakinta ne ga dukkan wanda ya ƙirƙiri ƙarya da kuma wanda ya tsaya ya yadata da watsata tsakanin mutane.
Ruwaito Hadisin ƙarya yana haramta akan wanda ya san kasancewarsa ƙarya ne, ko kuma ƙaryarsa ta rinjaya a zatonsa sai dai in ya kasance dan gargadi ne daga gare shi .