Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Dukkanin al'ummata za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi", suka ce: ya Manzon Allah, wa zai ƙi? ya ce: "Wanda ya bi ni zai shiga aljanna, wanda ya saɓa min to haƙiƙa ya ƙi".

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin al'ummarsa za su shiga aljanna sai wanda ya ƙi! Sai sahabbai - Allah Ya yarda da su - suka ce: Wa zai ƙi ya Manzon Allah?! Sai (manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya amsa musu cewa: wanda ya miƙa wuya ya bi Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - zai shiga aljanna, amma wanda ya saɓa bai miƙa wuya ga shari'a ba, to, haƙiƙa ya hanu daga shiga aljanna da ayyukansa munana.

فوائد الحديث

Lallai cewa bin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana daga biyayyar Allah, kuma saɓa masa yana daga saɓawa Allah.

Bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana wajabta aljanna, saɓa masa kuma yana wajabta wuta.

Albishir ga masu biyayya daga cikin wannan al'ummar, kuma cewa su dukkaninsu za su shiga aljanna, sai wanda ya saɓawa Allah da Manzonsa.

Tausayinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a

gareshi - ga al'ummarsa, da kwaɗayinsa a kan shiriyarsu.

التصنيفات

Annabinmu Muhammad SAW