Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu

Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane, to, yana daga cikinsu".

[Hasan ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya yi kamanceceniya da wasu mutane daga kafirai ko fasiƙai ko mutanen kirki - ta yadda zai aikata wani abu daga abin da ya keɓancesu daga aƙidu ko ibadu - to, yana daga cikinsu; domin kamanceceniya da su a zahiri yana kaiwa zuwa kamanceceniya da su a ɓoye, kuma babu kokwanto cewa kamanceceniya da mutane yana haifuwa ne daga sha'awarsu, kuma ya kan kai zuwa ga soyayyarsu da girmamasu da karkata zuwa garesu, wannan yana jan mutum zuwa ya yi kama da su har a ɓoye da ibada - Allah Ya yi mana tsari-.

فوائد الحديث

Gargaɗi daga kamanceceniya da kafirai da fasikai.

Kwaɗaitarwa a kan kamanceceniya da mutanen kirki da koyi da su.

Kamanceceniya a zahiri yana gadar da soyayya a ɓoye.

Mutum yana samun narko da zunubi gwargwadon kamanceceniya da nau'inta.

Hani daga kamanceceniya da kafirai a addininsu da al'adunsu waɗanda suka keɓanta da su, amma abin da bai zama irin hakan ba kamar neman sanin sana'o'i da makamancinsu, to, ba ya shiga a cikin hanin.

التصنيفات

Kamanceceniyar da aka Haramta