shin kana jin kiran Sallah idan aka kira, ya ce: Eh, sai ya ce: Ka amsa

shin kana jin kiran Sallah idan aka kira, ya ce: Eh, sai ya ce: Ka amsa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Ba ni da mai jagora da zai ja ni zuwa Masallaci, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da ya yi masa rangwane da ya yi Sallah a gidansa, sai ya yi masa rangwame, a lokacin da ya juya ya tafi, sai ya kira shi ya ce: shin kana jin kiran Sallah idan aka kira, ya ce: Eh, sai ya ce: Ka amsa.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Wani mutum makaho ya zo wurin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ya Ma’aikin Allah ! Ba ni da wanda zai taimaka min ya riƙe hannuna zuwa Masallaci a salloli biyar, yana son Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi masa rangwamen sallar jam’i, sai ya yi masa rangwamen, lokacin da ya juya ya tafi, sai ya kira shi, ya ce; Shin kana jin kiran Sallah? Ya ce; Eh, ya ce: Ka amsawa mai kiran Sallah.

فوائد الحديث

Wajibcin Sallar jam’i, domin rangwame ba ya kasancewa sai a abin da yake dole.

Faɗinsa: "Ka amsa". Wannan ga wanda yake jin kiran sallah, yana nuna Wajibcin sallar jam’i, domin asali a umarni shi ne Wajibci.

التصنيفات

Falalar Sallah cikin jama’a da Hukunce Hukuncenta