إعدادات العرض
Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu
Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu
Daga Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mubaya'a a kan ji da biyayya a halin rintsi da sauƙi, da farin ciki da baƙin ciki, da kuma nuna fifiko a kammu. Kuma kada mu yi wa ma'abota al'amari jayayya, kuma mu faɗi gaskiya a duk inda muke, ka da mu ji tsoron zargin mai zargi a al'amarin Allah.
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands සිංහල ไทย دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली Malagasy Italiano or ಕನ್ನಡ Oromoo Română Soomaali Српски Wolof Українська Moore Azərbaycan ქართული Magyarالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya riƙi alƙawari daga sahabbansa wajen jagorantuwa (biyayya) ga majiɓinta al'amura da shugabanni a halin sauƙi da wahala, da halin wadata da talauci, kuma duk ɗaya ne umarninsu ya kasance daga abin da rai yake so ne ko yake ƙi, kai ko da shugabanni sun yi babakere da dukiyar jama'a ko muƙamai ko wanin hakan a kan talakawa; to, dole ne a ji [maganarsu] a yi biyayya bisa sanannun abubuwa, kada a yi musu tawaye, domin fitina da ɓarna wajen yaƙarsu ita ce mafi girma, kuma mafi tsanani daga ɓarnar da za ta faru saboda zaluncinsu, yana daga abin da suka yi alkawari a kansa cewa za su faɗi gaskiya a kowanne wuri suna masu yi wa Allah ikhlasi cikin haka, ba sa jin tsoron wanda zai zargesu.فوائد الحديث
[Kyakkyawan] sakamakon ji da bi ga majiɓinta al'amura shi ne haɗuwar kan musulmai da watsar da rarrabuwa.
Wajabcin ji da bi ga majiɓinta al'amura in ba a saɓon Allah ba ne a cikin sauƙi da tsanani, da farin ciki da baƙin ciki da babakeren da za su yi.
Wajabcin faɗin gaskiya a duk inda muke, ba tare da mun ji tsoron zargin mai zargi ba cikin [al'amarin] Allah