Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar

Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar

Daga Abu Sirmah - Allah Ya yarda da shi - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya cutar Allah Zai haɗa shi da sakamakon cutar, wanda ya tsananta Allah Zai haɗa shi da sakamakon tsanantawar".

[Hasan ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi gargaɗi game ga shigar da cuta ga musulmi, ko riskar da wahala a gareshi a kowane al'amari daga al'amauransa; a ransa ko a dukiyarsa ko a iyalansa, kuma cewa wanda ya aikata hakan Zai yi masa sakayya, Zaiyi masa uƙuba daga jinsin aikinsa.

فوائد الحديث

Haramcin cutar da musulmi da riskar da wahala a gareshi.

Kamun Allah ga bayinsa.

التصنيفات

Hukunce Hukunce jivanta da barranta, Hukunce Hukunce jivanta da barranta