Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi

Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi

Daga Arfajah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya zo muku alhali al'amarinku gabaɗaya yana hannun mutum ɗaya (kanku a haɗe a ƙarƙashin shugabancin mutum ɗaya), kuma yana son ya tsaga sandarku, ko ya raba jama'arku, to, ku kashe shi ".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa musulmai idan suka haɗu a kan shugabancin mutum ɗaya, da jama'a ɗaya, sannan wani ya zo yana son ya yi jayayya da shi a shugabanci, ko yana son raba musulmai sama da kungiya ɗaya, to, ya wajaba su hana shi da kuma yaƙarsa; don tunkuɗe sharrinsa da kuma kare jinanen musulmai.

فوائد الحديث

Wajabcin ji da bi ga majinɓincin al'amarin musulmai in ba a saɓo ba, da haramcin yi masa tawaye.

Wanda ya yi tawaye ga shugaban musulmai da jama'arsu, to, yaƙarsa tana wajaba duk yadda matsayinsa yake a daraja da nasaba.

Kawaɗaitarwa a kan haɗa kai da rashin rabuwa da saɓani.

التصنيفات

Yi wa Shugaba Tawaye