Ya Allah duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tsananta musu, to, ka tsananta masa, duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tausasa musu, to, Ka tausasa masa

Ya Allah duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tsananta musu, to, ka tsananta masa, duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tausasa musu, to, Ka tausasa masa

Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana faɗa a cikin wannan ɗakin nawa : "Ya Allah duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tsananta musu, to, ka tsananta masa, duk wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amarin al'ummata sai ya tausasa musu, to, Ka tausasa masa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi mummunar addu'a a kan dukkanin wanda ya jiɓinci wani al'amari daga al'amuran musulmai ya kasance ƙarami ne ko babba, kuma duk ɗaya ne, wannan shugabancin ya zama shugabanci ne mai gamewa, ko wani bangare ne keɓantacce, kuma ya shigar musu da tsanani bai tausasa musu ba, cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai yi masa sakayya daga jinsin aikinsa ta yadda zai tsananta masa. Kuma cewa duk wanda ya tausasa musu ya sauƙaƙa al'amuransu cewa Allah Zai tausasa masa kuma zai sauƙaƙa al'amuransa.

فوائد الحديث

Yana wajaba a kan wanda ya jiɓinci wani abu daga al'amuran musulmai da ya tausasa musu gwargwadon iyawa.

Sakamako yana kasance daga jinsin aikin da aka yi.

Ma'aunin abinda ake lura da shi wajen tausayi da tsanani shi ne muddin dai bai saɓawa Al-Qur'ani da Sunna ba.

التصنيفات

Sharaxan Babban Shugabanci, Tausayinsa SAW