Fiqhun Mu’amala
50- Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yazo min don ya dubani shekarar Hajjin ban-kwana daga wani ciwo da yayi tsanani agareni,sai nace:Ya Ma'aikin Allah,hakika ciwo yakai inda yakai agareni kamar yadda kake gani,kuma ni Ma'abocin Dukiya ne,bamai gadona sai 'ya mace bana yi Sadaka da Biyu bisa Ukun Dukiyata ba?yace:a'a,nace:Rabi fa ya Ma'aikin Allah?yace:a'a,nace:Daya bisa Ukufa?yace:Daya bisa Uku,kuma Daya bisa Uku da yawa,hakika cewa kai kabar Magadanka Mawadata shi yafi akan kabarsu Talakawa suna rokon Mutane,kuma cewa kai ba zaka ciyar da wata ciyarwa ba kana mai neman Fuskar Allah face Allah ya baka lada da ita,hatta abinda zaka saka a Bakin Matarka.Yace:Nace ya Ma'aikin Allah zan barwa abokanaina a bayana?yace:Hakika cewa kai ba za'a barka ba ka aikata wani aiki da kake neman Fuskar Allah sai ka kara Daraja dashi da Daukaka,kuma watakila kuma idan aka barka har wasu su amfana da kai wasu kuma su cutu da kai,ya Allah ka cikawa Abokanaina Hijirarsu,kada ka juyar dasu a bayansu,sai dai sadauki shine Sa'ad Dan Khaula(yana yiwa Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-Rasa'i don ya Rasu a Makka)