إعدادات العرض
Fiqihu da Usulunsa - الصفحة 3
Fiqihu da Usulunsa - الصفحة 3
3- Mun kasance ba ma daukar kalar hanta-hanta da fatsi-fatsi a bakin komai bayan tsarki
4- Ki zauna gwargwadan abinda hailarki take riƙe ki, sannan ki yi wanka
6- Duk wanda yayi alwala ranar juma'a zai samu lafiya, kuma duk wanda yayi alwala shine mafi alkhairi
7- Wanka ranar Juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu
13- Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta
17- Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa
29- Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka
39- Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi
46- Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne
47- Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura
54- Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku
56- Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa
57- Idan Allah Ya kaddarawa bawa cewa zai mutu a wata kasa sai Ya sanya masa wata bukata zuwa gareta
58- Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
60- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai
61- Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu
63- Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa
65- Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati
66- Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna
68- Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna
70- Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita
71- ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata
87- Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji