Fiqihu da Usulunsa

Fiqihu da Usulunsa

43- Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara magana*: Lalle godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsari daga sharrin kawunammu, wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, ina kuma shaidawa [Annabi] Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicceku daga rai guda ɗaya, Ya halitta masa matarsa daga shi, daga su ya yaɗa maza da yawa da mata, Ku ji tsoron Allah Wanda ku ke magiya da Shi, (ku kiyaye) da zumunta, lalle Allah Ya kasance Mai kula da ku ne}. {Ya ku waɗanda ku ka yi imani ku ji tsoron Allah haƙiƙanin jin tsoronSa, kada ku mutu face kuna Musulmai}. {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku faɗi magana ta daidai, zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, duk wanda Ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta, rabauta mai girman gaske.

78- Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani *: "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".

96- "Lallai zan bai wa wani mutum wannan tutar Allah Zai yi buɗi ta hannunsa, yana son Allah da manzaonSa kuma Allah da manzonSa suna son shi". Ya ce: Sai mutane suka kwana suna tattaunawa a daran waye a cikinsu za'a ba shi ita, lokacin da mutane suka wayi gari sai suka yi jijjifi ga manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowanne su yana ƙaunar a ba shi ita, sai ya ce: "Ina Aliyu ɗan Abi Dalib?" sai aka ce : Shi ya manzon Allah yana ciwon idanu, ya ce: "Ku aike masa", sai aka zo da shi sai manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tofi a cikin (idanuwa) ya yi masa addu'a, sai ya warke kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, sai (Sayyidina) Aliyu ya ce: Ya manzon Allah, shin zan yake su ne har sai sun zama irinmu? sai ya ce: "Ka zarce a hankali har sai ka sauka a farfajiyarsu, sannan ka kira su zuwa ga musulunci, ka ba su labari da abinda yake wajaba akansu na hakkin Allah a cikinsa,@ na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen ni'imomi (rakuma)".